<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1) Wa ke samun albarka daga Ubangiji ?
 Wanda ya ke karanta
 Daga Litaffinsa.
 Har ya ji ya kiyaye
 Abin da ke ciki,
 Shi zai sami albarka
 Daga hannuwansa.

[V2]
 2) Wa ke samu albarka daga Ubangiji ?
 Wanda an gafarta
 Masa duk laifofinsa
 Ba lissafta gare
 Dukan muguntarsa.
 Allah zaya zubda su
 Cikin zurfin teku.

[V3]
 3) Wa ke samu alabarka daga Ubangiji ?
 Wanda ba ya biba ta
 Shawarar mugu ba.
 Ko a cikin hanyarsa
 Ba ya tsaya a ciki,
 Marmari da tunani
 Cikin shari'arsa.

[V4]
 4) Wa ke samu albarka daga Ubangiji ?
 Shi mai faɗin gaskiya
 Cikin zuciyarsa.
 Yana tafiya sosai
 Da aikin adalci
 Ba shi tsegume daɗai
 Ko zagin abokan shi.

[V5]
 5) Wa ke samu albarka daga Ubangiji ?
 Wanda a ke tsananta
 Sabo da adalci
 Ko mu kan sha wahala
 Sabo da sunansa
 Ladarmu mai girma ce
 Can a cikin sama.

[V6]
 6) Wa ke samu albarka daga Ubangiji ?
 Wanda ya ke jimrewa
 Lokacin jaraba
 Allah Mai aminci ne
 Ya yi hanya tsira
 Farin ciki mu ke yi
 Don ya ci nasara.

[V7]
 7) Wa ke samu albarka daga Ubangiji?
 Wanda ya ke jiransa
 Komowar ɗan Allah.
 Ya yi shirin zamansa,
 Ya bar bin duniya.
 Yesu yana zuwa kuwa
 Biɗan masu-binsa.</lyrics>
<title>Wa Ke Samun Albarka Daga Ubangiji? LW532</title>
<hymn_number>532</hymn_number>
</song>